7 Yuli 2023 - 11:15
Abubuwa Masu Muhimmanci Da Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Ranar Ghader

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya kawo maku takaitaccen bayani dangane da Ranar Idil Lahil Akbar Wato ranar Ghadeer Khum. Ranar da Manzon Rahama (Sawa) ya nada Imam Ali As A matsayin magajinsada zai jagoranci Al'ummarsa bayan baya nan.

1- Girman Ranar Idin Gadeer Ga Al’ummar Musulmi:

Ziyad dan Muhammad yace: Na shiga wajen Aba Abdullah As na ce da shi: shin musulmai suna da wani idi bayan ranar Juma’ah da ranar karama da babbar Sallah? Sai yace: kwarai, Ranar da Manzon Rahama SAWa ya nada Imam Ali Amiral Mu’umineen As” Misbahul Mutahajjid: 736

1-1 Manzon Allah SAWA Yace: “ Ranar Gadir Kum itace mafi falalar ranekun Idin al’ummata ita ce ranar da Allah anbatonsa ya daukaka da nada dan uwana Ali dan Abi Dalib jagora ga Al’umma, da zasu shiriya a hannunsa a bayana, kuma ita ce ranar da Allah ta’ala ya cika addini kuma a cikinta ne ya cikawa al’ummata ni’ima, kuma ya yarje masu musulunci a matsayin addini” Aamli Saduk: 125,h.8.

2- Idi Mai Cike Da Albarka:

Imam Sadik Yana Cewa: “ wallahi da mutane sun san hakikar falalar wannan rana da mala’iku sun yi musafaha da su a kowace rana sau goma, kuma kyauta da baiwar Allah ga mutumin da ya san wannan rana ba zai yiwu a kirga su ba” ( Misbahul Mutahajjid: 738

3- Ranar Kai Ziyara Ga Yan Uwa Mu’uminai

Imam Ali Dan Musar Ridha As Yace: duk wanda ya ziyarci mumini Allah zai shigar da haske saba’in ciin kabarinsa kuma ya yalwata cikin kabarinsa kuma mala’iku dubu saba’in ke zasu na ziyartarsa a kowace rana suna masu yi masa bushara da aljannah” (Iqbalul A’amal: 778)

4- Muhimmiyar Sallah A Ranar Gadir

Duk kan wanda yayi sallah raka’a biyu a ko wane lokaci yaso amma mafi soyiwa, gab da lokacin rana tazo tsakiya, itace sa’ar da aka kafa Imam Ali Amiral Mu’umineen As ga a’umma a matsayin jagora a Gadir Khum... to zai kasance kamar wanda ya halarci wannan ranar”. (Wasa’ilishi Shia: 5, 225, p,2).

5- Matsayin Imam Ali As Daga Bakin Manzon Allah SAWA

Manzon Allah SAWA: “ daga Jabir dan Abdullahil Ansary yace: naji Manzon Allah SAWA yana cewa ga Ali dan Abi Dalib AS,Ya Ali! Kai dan uwana ne kuma wasiyana kuma magajina kuma khalifana ga al’umma a rayuwata da bayan nayi wafati , masoyinka masoyina ne, makiyinka makiyina ne abokin gabarka abokin gabata ne” ( Aamalis Saduk: 124: j:5)

6- Ali Shi Ne Magajin Annabi {SAWA}:

Manzon Allah yace: Ya kai Ali ni ne birnin ilimi kai ne kai ne kofarta, kuma ba’a shiga birni birni sai ta kofa... kai ne limamin al’ummata kuma khalifana gareta a bayana, wanda yayi maka biyayya ya rabauta, wanda ya saba maka ya tabe, kuma wanda ya shugabnatar da kai ya yaci riba, wanda ya yaki binka yayi asara”. Jamiil Akhbar: 52, j, 9).