29 Agusta 2022 - 17:40
Tafarkin Gwagawarmayar Musulunci a kasar Labanon Tafarkin Imam Khumaini (RA) Ne.

Sheikh Zuhair Jaeed, kodinetan kungiyar Islamic Action Front na kasar Lebanon, ya taya babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah murnar cika shekaru 40 da kafa kungiyar Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: Sheikh Zuhair Jaeed, jami'in gudanarwa na kungiyar Islamic Action Front na kasar Lebanon, ya taya babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah murnar cika shekaru 40 da kafa kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon.

Inda ya yi nuni da cewa: Mun yi imani da wannan tafarki na Musulunci, wanda shi ne tafarkin Imam Khumaini (RA), mun yi riko da tafarkin gwagwarmaya, kuma muna daukar gwagwarmaya a matsayin hanya daya tilo na daukaka, daraja, karama, da jagoranci na 'yantar da dukkan kasashen yankunan da aka mamaye na Lebanon da yankin gaba daya.

Sheikh Jaeed ya yi furuci ga Sayyid Hasan Nasrallah inda ya ce: Kai ne alami kuma abin koyi ga dukkan masu fafutukar gwagwarmaya a Musulunci ta kowace fuska.


342/