Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Rusial-Yaum ta nakalto ministan yana fadar haka ne a yau laraba 25 ga watan Mayu, wanda ya zo dai dai da ranar da kungiyar Hizbullah ta sami nasarar korar sojojin Isra’ila daga kasar Lebanon a shekara ta 2000.
Ministan ya kara da cewa nasarar da kungiyar hizbulla ta samu a shekara ta 2000 kan sojojin mamaya na yahudawan sahyoniya a kudancin kasar Lebanon ya bude kofar nasarorin da ta ci gaba da samu a kan HKI daga cik har da yakin shekara ta 2006 inda mayakan kungiyar suka sami nasarar fatattakar sojojin Isra’ila wadanda suke son sake mamayar kasar.
Amma bayan yaki na kwanaki 33 ba tare da nasara ba, da kuma hasarori masu yawa na rayuka da kayakin yakin, yahudawan sun bada kai sun kuma amince da dakatar da budewa juna wata. Tun lokacin ya zuwa yanzu shekaru 15 kenan sojojin HKI basu sake mafarkin mamayar kasar Lebanon ba.
342/