24 Mayu 2022 - 19:35
Taiwan : Amurka Na Wasa Da Wuta Ne, Inji China

Kasar China ta mayar da martani kan furicin shugaban Amurka Joe Biden, na cewa za ta tura sojoji domin kare tsibirin Taiwan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake mayar da martani kan kalammam na Biden, kakakin ofishin kula da harkokin waje na Taiwan majalisar kasa ta China, ya ce Amurka na wasa da wuta ne, kuma zata kona kanta da kanta idan ta yunkuri tunkarar China game da batun na Taiwan.

Amurka dai ta bakin Shugaban kasar ta ce za ta tura sojoji domin kare Taiwan idan China za ta mamaye tsibirin.

Biden ya bayyana a yayin ziyara da ya kai Japan, cewa Amurka da kawayenta ba za su bari hakan ya faru ba bisa la'akari da bin da ya faru a Ukraine.

342/