Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jawabin farko da yayi bayan sanar da sakamakon zaben yan majalisa da aka yi a kasar Lebanon sayyid nasrollah ya cewa duk wata barazana da tsoratarwa da Alummar kasar da aka yi domin juya baya ga yan gwagwarmaya bai yi tasiri ba, ya ce kujerun da kungiyar ta samu a zaben da aka yi babban nasara ce da ke tabbatar da yadda farin jininta ke karuwa .
Da yake ishara game da zargi mara tushe da ake yi na tsoma bakin iran a batun zaben kasar yace ba’a taba ganin Jakada ko wani ma’aikacin ofishin jakadancin Iran da ya sa baki a zaben kasar ba, amma kowa ya shaida yadda ofishin jakadancin Amurka da jakadan Saudiya suke katsa landam a harkokin zabe dumu -dumu a kasar.
342/