Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya Asabar dai mutane 15 suka rasa rayukansu a duk fadin kasar. Sannan gwamnatin kasar ta kafa dokar hana fita a duk fadin kasar don hada yaduwar cutar da kuma gano wadanda suke dauke da ita tun basu yada ta ga wasu ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, har yanzun gwamnatin Pyongyang bata nuna alamun zata karbi tallafin alluran riga kafin cutar wadanda kasashe da dama suka gabatar mat aba.
Tun ranar 12 ga watan Mayun da muke ciki ne gwamnatin Pyongyang ta kafa dokar hana fita a duk fadin kasar, sannan shugaban kasar Kim Jong-un ya bukaci a gudanar da gwaje-gwajen cutar da gaggawa don ganin an shawo kan wannan bala’in da ya fadowa kasar.
Shugaban ya fadawa majalisar jam’iyyar ma’aikata ta Korea ta Arewa kan cewa yaduwar cutar a kasar Korea ta arewa babbar musiba ce wacce dole ne a hada kai da gaggawa don yakar ta.
342/