Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar muryar JMI ta nakalto majiyar tana cewa tun ranar 2 ga watan Afrilun da ya gabata ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, amma gwamnatin kasar Saudiya da kawayenta sun ki aikin da sharuddan tsagaita bude wuta, wanda ya hada da barin jiragen sama su sauka su tashi a birnin San’aa babban birnin kasar, sannan sun hana wasu jiragen ruwa dauke da makamashi isa tashar jiragen ruwa na Hudaida kamar yadda aka amince a lokacin yarjejeniyar.
342/