4 Mayu 2022 - 18:48
​Abdollahian: Ana Ci Gaba Da Tattaunawar Vienna Ta Hanyar Musayar Rubutattun Sakonni

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya tabbatar da cewa ana ci gaba da shawarwarin Vienna ta hanyar musayar sakwanni a rubuce a tsakanin bangarorin da ke halartar tattaunawar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amir Abdollahian ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a yau da wakilin tashar Al-Masirah ta kasar Yemen, inda ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kasancewa a kan bakanta na goyon bayan al’ummar Falastinu, da kuma goyon bayan kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar.

Yayin da yake ishara da shawarwarin Vienna, ya ce: Ba a dakatar da yin shawarwarin ba, amma ana ci gaba da tattaunawa da Amurkawa ta hanyar musayar sakonni a rubuce domin kawar da takunkumin da aka sanya wa Iran.

Ministan harkokin wajen kasar ya ci gaba da cewa: Burinmu a wannan shawarwarin shi ne samun yarjejeniya mai karfi kuma mai dorewa, kamar yadda muka yi kira ga bangaren Amurka da su kasance da kyakkyawar fahimta, domin soke takunkumin da aka sanya a fannoni daban-daban.

Ya bayyana imaninsa cewa bangaren Amurka ya fahimci jajayen layukan Iran, ya kuma jaddada cewa Tehran za ta ci gaba da yin shawarwari, kuma da zarar an cimma matsaya, wakilin Iran a wannan shawarwarin zai aiwatar da sauye-sauyen karshe a yarjejeniyar.

Kalaman na ministan harkokin wajen na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya sanar da cewa, za a iya cimma yarjejeniya a birnin Vienna na farfado da shirin hadin gwiwa da kuma kawar da takunkumin da aka sanya wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

342/