20 Afirilu 2022 - 13:55
UAE Ta Gayyaci Jakadan Isra'ila Kan Rikicin Masallacin Qudus

Ajiye talata ce hadaddiyar daular larabawa ta gayyaci jakadan Isra’ila a abu dabi inda a bayyana mata rashin amincewarta afili da kuma yin tir da abin da ke faruwa a masallacin kudus

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ana ta bangaren karamar ministar kula da huldodi na kasa da kasa Reem Bin Ibrahim Alhashimi ta jaddada bukatar da ake da shi na kawo karshen rikicin da ke faruwa a masallacin Kudus, tare da bada kariya ga masu ibada, da kuma mutunta hakkokin falasdinawa na gudanar da ayyukan addininsu da kuma dakatar da aiwatar da duk wani abun da zai kawo rikici a birnin Qudus.

Haka zalika ta kara jaddada bukatar da ake da shi wajen samar da yanayi da ya dace da zai sa a koma tattaunawa da nufin samar da zaman lafiya na adalci da kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai dake da iyaka tun na shekara ta 1967,mai hedkwata a birnin Kudus, da ya dace da dokokin da aka amince das u da kuma kudurin samar da sulhu da kungiyar hada kan ksashen larabawa suka fitar.

342/