17 Afirilu 2022 - 19:02
Afganistan : Mutum 47 Suka Mutu A Harin Pakistan

Hukumomin Afganistan sun ce alkalumman mutanen da suka mutu a harin Pakistan a gabashin kasar sun kai 47.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwa ta ce fararen hula 41 akasari mata da yara ne suka mutu, kana wasu 22 suka jikkata a harin saman da sojojin Pakistan suka kai a kusa da layin Durand dake lardin Khost, kamar yadda Shabir Ahmad Osmani Darektan yada labarai na yankin ya shaidawa kamfanion dilancin labaren France-Presse.

Ko baya ga shi din akwai wasu hukumomin yankin biyu da suka tabbatar da labarin.

Bayan dai aukuwar harin gwamnatin Afganistan, ta gargadi kasar Pakistan akan keta hurimin nata.

Tana mai kira ga Pakistan data kaucewa hakan don kada a jefa yankin cikin wani rikici.

342/