8 Afirilu 2022 - 20:22
Iran Ta ce Akwai Siyasa A Kudurin MDD Na Dakatar Da Rasha Daga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam

A cikin wani bayani da Majid Takht ravanchi jadan dindin din na kasar Iran a majalisar dinkin duniya ya fitar game da kudurin da majalisar dinkin duniya ta fitar na dakatar da kasar rasha daga hukumar kare hakkin bil dama ta majalisar siyasa ce kawai wanda yake nuna irin nuna son kai din dake cikin majalisar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya Alhamis ce hukumar kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya sanar da dakatar da kasar rasha daga cikinta, saboda zargin da ake mata da keta hakkin bil adama da dakarun kasar suka yi a kasar Ukrain

Kimanin kasashen 128 ne suka kafa kuri’ar amincewa da kudurin yayin da kasashe 9 suka kada kuri’ar nuna rashin amincewa inda kuma kaashen 35 suka kasance a amatsayin yan baruwanmu,

Tun kafin kada kuri’ar kasar rasha ta yi barazanar cewa duk kasar da ta kada kuri’ar amincewa ko kuma yar ba ruwanmu da hakan zai bawa Amurka damar ganin an dakatar da ita da hukumar kare hakkin dan Adama za ta dauketa a matsayin yar adawa , kuma zata biya farashi a dangantakar dake tsakaninta da ita.

342/