Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Akwai dai rashin tabbas game da adadin rayukan da aka rasa yayin bata-kashin, ko da yake alkaluma na nuna wadanda aka kashe din sun haura mutum dari.
Da yake karin haske game da al’amarin, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq ya ce “Jami’an wanzar da zaman lafiya da abokan aikinsu, sun yi matukar damuwa da samun rahoton kisan fararen hula, suna kuma aiki tukuru wajen tabbatar da hakikanin abun da ya faru, ciki har da tantance ko an keta hakkokin bil adama yayin tashin hankalin da ya auku”.
342/