2 Afirilu 2022 - 11:25
An Sanar Da Fara Azumin Watan Ramadan A Wasu Kasashen Musulmi Na Duniya A Yau Asabar

A jiya ne aka sanar da ganin jinjirin watan Azumin watan ramadana mai alfarama a wasu kasashen musulmi inda yake yau Asabar daya ga watan ramadana. Kasashen Najeriya Saudi Arebiya Qatar, Kuwait, Hadaddiyar daular larabawa, yankin Kurdawa na kasar iraki suna daga cikin kasashen da suka tashi da Azumin watan Ramadan,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sai dai wasu kasashen kamar Iran da masarautar Brunei sun sanar da gobe lahadi a matsayin daya ga watan Ramadan mai alfarma, wato asabar ne ranar karshe ta watan Sha’aban a wajen su,

A wata sanarwa da ta fito daga ofishin jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi Imam Khamna’I ya nuna cewa gobe lahadi 3 ga watan Aprilu shi ne ranar Farko na watan Ramadan a kasar, haka suma kasashen Oman, Malesiya, Indunusiya da ma wasu kasashen su ma gobe ne daya ga watan tamadan.

342/