Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Taron mai taken “Afghanistan da makwabtanta”, da ya gudana a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya samu halartar ministocin harkokin waje, da wakilai daga kasashen Pakistan, da Iran, da Rasha, da Tajikistan, da Turkmenistan da Uzbekistan.
Bangarorin na musanyar ra’ayoyinsu, kan batutuwan da suka shafi matsa kaimi ga samun dawwamaman zaman lafiya a Afghanistan, da tallafa wa al’ummar kasar da dai sauransu.
taron tattaunawa, na kuma samun halartar Amir Khan Mottaki, mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan, da ministocin harkokin wajen kasashen Indonesiya, da Qatar.
342/