Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Babban jami'in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a lokacin da ya isa kasar Sin a ranar Larabar nan, a yayin da yake jagorantar wata babbar tawaga ta siyasa domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen da ke makwabtaka da Afghanistan karo na uku.
Ya kara da cewa Tehran da Beijing, "suna fatan ganin kasar Afganistan mai zaman lafiya mai ci gaba, wacce ke hulda da makwabtanta," in ji shi.
Pakistan da Jamhuriyar Musulunci ne suka dauki nauyin taron karo na farko da na biyu a shekarar da ta gabata.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce "Afganistan ta cancanci karin kulawa a bangaren kasashen duniya."
Kasar Afghanistan dai ta fada cikin tashin hankali tun bayan da kungiyar Taliban da ta taba mulkin kasar ta Afganistan daga shekarar 1996 zuwa 2001, ta sake karbar mulki a ranar 15 ga watan Agustan bara, daga bisani kuma ta sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya.
Farfadowar kungiyar ta zo ne a cikin gaggawa da rudani na ficewar sojojin Amurka daga kasar da ke tsakiyar Asiya.
Daga nan sai Amurka da kawayenta suka dakatar da tallafin kudi da suke baiwa Afganistan, lamarin da ya kara rura wutar rikicin 'yan gudun hijira da ya shafi makwabtan Afganistan.
342/