Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, kafin hakan daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun shiga hubbaren a wajen garin Nablusa a jiya talata tare da rakiyar jami’an tsaron yahudawa, inda suka wulakanta wurin da yahudawa da musulmi da kiristoci gaba daya suke girmamawa.
An fara tashin hankali ne a wurin a yau Laraba bayan da Falasdinawa suka fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da wulakatanta wurin da kuma kissar wasu matasa Falasdinawa 3 a yahudawan suka yi a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Da dama daga cikin falasdinawan suna zubar da hawaye saboda hayaki mai sa hawaye da aka jefa masu, a yayinsa wasu kuma albarusan ruba na yahudawan sun ji masu rauni.
342/