14 Maris 2022 - 17:43
Yan Majlisar Iran 160 Sun Bukaci Masu Shiga Tsakani Kada Su Yarda Da wa’adin Wucin Gadi A Vieanna

A wani bayani na kadin guiwa da yan majalisar shawarar Musulunci na kasar iran suka fitar a yau lahadi sun bukace masu shiga tsakanin na kasar a tattaunawar Veanna na cire mata takunkumi kada su dagara da wa’adin wucin gadi , sun bukaci da su kare maslahar alummar kasar kuma su dake kan abubuwa da aka gindaya a matsayin jan layi ne a tattaunawar

Rikicin kasar Rasha da Ukrani ya sa kasashen turai tsananin bukatar samar da makamashi daga kasar Iran, sai dai bai kamata a samu raguwar farashin danyen mai ba kafin Amurka ta biyawa Iran dukkan hakokinta da aka tabbatar mata ba.

Tawagar dake shiga tsakanin ta nuna cewa akwai bukatar Amurka ta biya diyya kan asarar rasa rayuka da ta jawo wa kasar Iran, kuma dole na cire takunkumin ya zama cikakke da zai yi tasiri kuma ya kare maslahar alumma. Kuma ya kasance a rubuce ba a fatar baki ba.

Daga karshe an bukaci Tawagar masu shiga tsakanin da ta su bukaci wadatattun lamuni na Tattalin arziki kimiyya da fasaha siyasa daga Amurka da kuma ba da tabbacin cewa Amurka ba za ta fice daga cikin yarjejeniyar ba bisa ka’ida ba kamar yadda tayi a baya.

342/