Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dubban alummar kasar Yamen ne suke bukatar abinci ,manfetur da dangoginsa sakamakon matsalar yaki da kasar ke ciki, amma Dakarun hadin guiwa da saudiya ke jagoranta suna sace miliyoyin gangar mai na kasar yamen da aka kwace aka hana shigar da shi kasar.
Ko a jiya litinin ma Dubban Alummar kasar Yamen sun yi zanga-zangar nuna adawa da rike man fetur din kasar da dangoginsa karkashin jagorantar Amurka, kuma sun yi Tir da killace kasar da Saudiya da Amurka suka yi,
Daga karsher masu zanga-zangar sun rika rera taken neman yanci da kuma yin tir da gum da baki da majalisar dinkin duniya take yi game da laifukan yaki da kawance da saudiya ke jaoranta bisa goyon bayan Amurka suke tafkawa a kasar.
342/