8 Maris 2022 - 15:47
Jamus Ta Yi Watsi Da Shawarar Sanyawa Rasha Takunkumi A Fannin Albarkatun Mai

Ministocin kudi da kuma na harkokin wajen kasar Jamus, sun yi watsi da shawarar da wasu kawayensu na turai da Amurka suka fara yi na a sanyawa Rasha takunkumi a fannin albartun mai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock, ta ce wannan tunanin ba shi ne mafita ba, kuma kada a yi tsammanin irin wannan matakin zai dakatar da tabkokin yakin Rasha ba.

Sama da rabin iskar gaz da Jamus ta dogara da shi tana shigar da shi ne daga Rasha, sannan kashi 42% na man fetur din ta da kuma kwal daga Rasha ne.

Rikicin na Rasha da Ukraine, a wannan Litinin rikicin kara ya girgiza kasuwannin duniya musamman farashin man fetur, zinari da kuma mummunar faduwar hannayen jari a Asiya.

342/