3 Maris 2022 - 17:33
Iran Ta Bayyana Rike Kudaden Afghanistan Da Amurka Ta Yi Da Cewa Bai Dace Ba

Mataimakiyar jakadan Iran a MDD, Zahra Irshadi ta bayyana cewa; Kudaden Afghanistan da aka rike na al’ummar kasar ne, don haka dole ne a saki kudadensu domin a sake farfado da tattalin arzikin Afghanistan da ceto da rayuwar mutanen kasar.”

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Zahra Irshadi ta cigaba da cewa; Ko kadan bai dace ba a shigar da siyasa a cikin batun dukiyar mutanen Afghanistan ko kafa musu wani sharadi.

Mataimakiyar jakadan Iran din a MDD ta kuma ce; Kasar Afghanistan tana fuskantar kalubale mai girma ta fuskar tabarbarewar rayuwar mutane, haka nan kuma koma bayan tattalin arziki.

A kasar ta Afghanistan da akwai mutanen da suka kai miliyan 20 ko kuma rabin al’ummar kasar da suke da bukatuwa da taimako.

Jawabin mataimakiyar jakadan ta Iran a MDD ya zo ne a lokacin taron kasa da kasa da ake yi a MDD dangane da kasar Afghanistan.

Wani kalubanen da kasar take fuskanta shi ne na hare-haren ta’addanci na kungiyar Da’esh, da ya zuwa yanzu ta kai hare-hare da suka kai 152 a cikin gundumomi 16 a tsakanin watan Ogusta zuwa Disamba na 2021 kadai.

342/