Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ali Bagheri Kani, ya dawo Iran ne a ranar Laraba, domin tuntubar mahukuntan kasar game da wasu batutuwa.
Kafin hakan ya yi kira ga kasashen yamma dasu dauki matakai domin a kai ga cimma matsaya a tattaunawar da ake a Vienna.
Tattaunawar ta Vienna ta kai wani matsayi mai mahimmanci a cikin 'yan kwanakin nan, kuma dukkan masu ruwa da tsaki a tattaunawar na jiran shawarar da Amurka za ta yanke.
A makon da ya gabata mai jagorantar tawagar ta iran a tattaunawar, Mista Bagheri, ya ce sun kwashe makonni na tattaunawa mai zurfi inda aka kasance kusa da cimma matsaya.
342/