25 Faburairu 2022 - 20:09
Abdollahian : Rikicin Ukraine Ya Samo Asali Ne Daga Tsokanar NATO

Iran, ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa, rikicin Ukraine ya samo asali ne daga tsokanar kungiyar tsaro ta NANO.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hossein Amir-Abdollahian, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis cewa, rikicin Ukraine ya samo asali ne daga ayyukan tsokana na kungiyar tsaro ta NATO, a daidai lokacin da Rasha ta kaddamar da farmakin soji kan Ukraine.

Amma babban jami’in diflomatisyya na Iran, ya ce “Ba ma ganin daukar yaki a matsayin mafita, ya kamata a nemi hanyar tsagaita bude wuta’’

342/