24 Faburairu 2022 - 14:43
​Najeriya: Jam’iyyar APC Ta Rarraba Shugabancin Jam'iyyar A Tsakanin Shiyoyi 6 Na Kasar

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta rarraba mukamai na shugabancin jam’iyyar saboda zabubbukan shekara mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Premium times ta bayyana cewa Jam’iyyar ta yi haka ne bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar da shugaban kasa a jiya Laraba.

Labarin ya nakalto gwamnan jihar Kaduna Mr Ahmed El-Rufa’ii yana cewa dukkan mukaman da suke arewa a wannan karon zasu koma kudanncin kasar sannan na kudanci kuma zasu koma arewacin kasar.

El-Rufae ya ce daga ciki shugabancin Jam’iyyar zata dawo shiyar arewa ta tsakiya, wato Jihohin Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, da kuma Plato.

Labarin ya kara da cewa shiyan kudu maso kudu zata samar da sakataren jam’iyya ta kasa, shugaban matan Jam’iyya ta kasa, da kuma mataimakin jami’I mai kula da jin dadin jam’iyyar. Kuma shiyar ta kunshi jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da kuma Rivers.

342/