Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi minitsan harkokin wajen Iran ya ce Ba zamu ketara wani jan layi ba a cikin kowanne hali duk da shiga mataki mafi tsauri da aka yi a tattaunawar da ake yi a vianna tsakaninta da kasashen turai kan cire mata takunkumi
Yace muna da kyakkyawa fata game da tattaunawar da ake yi vianna, kuma mana fatan ganin an warware sauran abubuwa masu muhimmancin da ake da sabanin akansu amma a lokaci daya kuma muna duba muhimmanci tattaunawa ta kasance mai amfani yadda alummar iran za su amfana da ita.
Daga karshe ya nuna cewa ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninm manyan masu shiga tsakani na kasar iran da wakilan kasashen turai 5 a vianna, kuma ana musayar takarda tsakani wakilan kasar Iran da na Amurka ta hanyar Mora wakilin kungiyar tarayyar turai a wajen zaman.
342/