Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban ya fadi haka ne a lokacin ganawarsa shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang a gefen taro karo na 6 na shuwagabannin kasashen dake fitar da iskasar Gas da aka kammala a birnin Doha na kasar Qatar, ya kara da cewa bayan da dinbin Arzikin da Allah ya basu kasashen Afrika suna da mutane masu aiki turku wanda zasu taka muhiimiyar rawa wajen ci gaban Nahiyar
Har ila yau ya kara da cewa kasashen turai suna kwashe shekaru suna wawason dinbin albarkatun kasa da Allah ya huwace musu da ma’aka a nahiyar don ci gaba da kare tsarinsu an mulkin mallaka da suka canza masa salo sabanin yadda suke yi a da.
A nasa bangaren shugaban kasar Equatorial Guinea ya bayyana Iran a mastsayin babbar kasa , yace kasashen turai suka yi wa nahiyar mulkin mallaka na tsawon shekaru, a halin yanzu nahiyar tana bukatar kasashe irin Iran domin yin aiki tare da yin amfani da albakatun kasa da suke dashi don amfanin mutanen Afrika
342/