16 Faburairu 2022 - 19:43
Hukumar Zabe A Najeriya INEC Tayi Rijistan Sabbin Masu Zabe Fiye Da Miliyan Biyar

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan, inda ya nuna cewa ya zuwa watan fabreru da muke ciki hukumar ta samu nasarar yiwa sabbin masu zabe miliyan 5.8 rijistan sunyensu a ci gaba da kokari da take yin a ganin ta yi wa kowa rijister sunansa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Har ila yau y akara da cewa kimanin mutane miliyan 1.3 daga cikin masu rijister suka yi tasu rijistar ta hanyar yanayar gizo, yayin da kuma miliyan 1.84 kuma suka yi ido da ido a wuraren da hukumar ta kebe don yin rijister. Muma miliyan 1.6 maza ya yin da kuma 1.5 mata ne sau kuma 27543 Nakasassu ne

Kimanin mutane miliyan 9.9 da suka yi rijistar sun bukaci a canza musu wurin zabe ko kuma an canza musu katin zaben, daga karshe hukumar ta INEC ta yi la’akari da cewa mutum miliyan 5.2 da su ka bada buƙatar su maza ne, sannan miliyan 4.6 mata ne, yayin da 95,138 naƙasassu ne.

342/