Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto Conovey yana fadar haka a jawabin hadin giwa da ya hada shi da tokwaransa na kasar Iran Husain Amir Abdullahiyan a safiyar yau a nan birnin Tehran.
Simon Conovey ya kara da cewa kasarsa ce ta jagorancin batun samar da kudurin MDD mai lamba 2231 wanda ya ke tabbatar da yarjejeniyar Nukliya ta kasar Iran wacce aka fi sani da JCPLOA, sannan ya fahinci irin girman matsin lamaban da takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Iran take wa mutanen kasar.
Ministan ya kara da cewa raya yarjejeniyar JCPOA zai amfani kasar Iran kuma zai bude kofofin sabbin yarjeniyoyin fahintar Juna tsakanin kasashen yamma da Iran. Sannan ya kammala da cewa sun tattauna batuituwa da dama da Amir Abdullahiyan, wadanda suka hada da kasashen Yemen, Lebanon, Siriya da kuma Afganistan.
342/