13 Faburairu 2022 - 13:42
Ministan Harkokin Wajen Kasar Mali Na Ziyara A Iran

Ministan harkokin wajen kasar Mali, Abdoulaye Diop, ya fara wata ziyara a birnin Tehran na Jamhuriyar musulinci ta Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Yayin ziyarar tasa Mista Diop, ya gana da takwaransa na Iran, Amir Abdolahian, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar kasashen biyu.

Mali da Iran dai na da dadadiyyar alaka a tsakaninsu.

Gwamnatin Iran dai ta jadadda aniyarta na kara karfafa alakarta da kasashen nahiyar Afrika.

024