12 Faburairu 2022 - 16:23
Libiya Ta Sake Fadawa Rudani, Bayan Da Ta Tsinci Kanta Da Firaministoci Guda Biyu

A Libiya a shiga wata sabuwar dambarwa bayan da kasar ta tsinci kanta da firaministoci guda biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Hakan dai ya biyo bayan da majalisar yankin Tobrouk ta nada tsohon ministan cikin gida Fathi Bachagha, a mukamin, bayan cimma wata yarjejeniyar siyasa a tsakanin bangarori da dama na yankin cikin har da gungun masu dauke da makamai ciki har da dakarun dake biyaya ga Janar Khalifa Haftar.

A nasa bangare kuwa Abdel Hamid Dbeibah, wanda ke samun goyan bayan MDD, ya ce shi kam ba zai mika mulki bag a wata gwamnatin wacce ba’a zaba ba.

Tuni dai aka fara nuna damuwa game da makomar kasar bayan kasa shirya zabubukan da ake kallo masu mahimmanci a gare ta a watan Disamba da ya gabata.

Dama Libiya ta saba fadawa irin wannan dambarwar inda ko a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 ta fuskanci shugabancin na gwamnatoci guda biyu.

A wannan Juma’ar babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bukaci dukkan bangarorin dasu ci gaba da samar da yanayi na zaman lafiya a kasar da kuma sgirya zabubuka cikin lokacin da ya tsawaka.

342/