8 Faburairu 2022 - 14:03
Zakarun Gasar Kwallon Kafa Na Afrika Sun Isa Gida

Tawagar kwallon kafa ta Senegal, wacce ta dauke kofin kwallon kafa na AFrika na bana, ta isa gida inda ake ci gaba da murnar nasara ta farko da kasar ta samu ta dauke kofin a cikin shekaru 60.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gwamnatin kasar dai ta ayyana wannan ranar a matsayin hudu ga kowa domin ci gaba da murnar nasarar.

Shugaban kasar Macky Sall, ya tarbi tawagar ‘yan wasan na Teranga a fadarsa inda ya mika masu tutar kasar.

Senegal dai ta dauke kofin ne bayan doke Masar a bugun daga kai sai mai tsaron gida 4-2.

Wannan ya baiwa kasar damar doke kofin a karon farko, bayan fafatawar wasan karshe a 2002 da 2019.

342/