Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, a ranar Juma’a ne kungiyar Hashdush Sha'abi ta kasar Iraki ta fara shirinta na tsaro domin zuwa ziyarar hubbaren Imam Hadi (AS) da ke birnin Samarra a lardin Salahuddin.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, jami'an Hashdush Sha'abi sun fara aiwatar da shirin tsaro na tabbatar da tsaron maziyarta Haramin Imam Hadi (AS) da ke birnin Samarra.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamandan Hashdush Sha'abi da ke birnin Samarra, ya jibge dakarunsa a kan hanyar Bagadaza zuwa Samarra, tare da ware mayaka 3,500 da motocin soji 600 tare da na’urorin soji na zamani domin samar da tsaro ga maziyarta a Samarra daga ciki da wajen Iraki. .
Hashd Shaabi ta bayyana cewa, tuni aka fara gudanar da aikin tabbatar da tsaro domin gudanar da bincike a kewayen da kuma tsakiyar birnin na Samarra domin dakile duk wani abu da ka iya kawo tabarbarewar yanayi, sannan kuma jami'an tsaron sun bincike dukkan tsibiran da kogin da ke daura da haramin Imam Askari (as).
342/