31 Janairu 2022 - 19:23
Kasar Labanon Ta Lalata Cibiyar Leken Asirin Israila Guda 15

Bayan yakin kwanaki 33 a shekara ta 2006 wanda kungiyar HIzbullah a yi nasara akan Isra’ila , wannan yasa sojojin da jami’an leken Asirin Isra’ila ta kara yawan ayyukan lekan Asiri da tsaro a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahoton da Jaridar Al-akhbar ta fitar ya nuna cewa jami’an tsaron cikin gidan kasar labanon sun samu nasarar tarwasta wasu cibiyoyin leken asiri na Isra’ila guda 15 kowanne daga cikinsu yana gudanar da ayyukan lekan Asiri a bangarori daban daban tsakanin labanon da siriya

Jami’an tsaron cikin gidan kasar Labanon sun gudanar da gagarumin samame mai cike da tarihi kan cibiyoyin tsaron Isra’ila , inda acikin makwanni 4 sun samu bayanai da suka kunshi mutane da dama da ake zargin da hannun kai tsaye ko ta bayan fage wajen yi wa Isra’ila leken Asiri

342/