Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amir Abdullahiyan ya yi tattaunawar da Antonio Guterress akan abubuwan da suke fareuwa a cikin kasar Yemen, inda ya jaddada cewa matsayar jamhuriyar musuluncin ta Iran shi ne son ganin an sami zaman lafiya da kawo karshen yaki.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Iran ya bukaci ganin MDD ta taka gagaruwar rawa domin kawo karshen wahalhalun da alúmmar Yemen suke ciki.
Dangane da halin da kasar Afghanistan kuwa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyanawa babban sakataren MDD yadda a cikin watannin bayan nan, jamhuriyar musulunci ta Iran ta kabi bakuncin ‘yan gudun hijira 800,000 daga Afghanistan.
Wani sashe na ttataunawar ya tabo batun tattaunawar da ake yi a birnin Vienna dangane da yarjejeniyar Nukiliya.
342/