Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jakadun kasahen biyu dukkan su sun amince cewa musayar kudade tsakanin kasashen ta yi kasa sosai , Barazil tana daga cikin manyan abokan huldar kasuwanci na kasar Iran a yankin latin Amurka, huldar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu ta kai tad ala bilina 2.5 a shekara ta 2021 da ta gabata, duk da kalubalen da suke fuskanta na takunkumin Amurka kan iran da kuma Annobar cutar korona virus.
A shekarar da ta gabata cibiyar hadin guiwa ta kasuwanci tsakanin Iran da Brazin ta bude ofishinta a birnin Sao Polo , kuma yanzu haka kasashen biyu suna shirin kara fadada huldarsu a bangaren musayar kudade ta hanyar bankuna, idan shirin ya tafi kamar yadda ake tsara huldar kasuwanci tsakaninsu za ta haura dala biliyan 10 nan da shekara ta 2025.
342/