Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto Yakubu yana fadar haka a taron watanni uku-uku na wannan shekara tsakaninta da jam’iyyun siyasa kamar yadda aka saba a Abuja.
Kafin haka dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki ya sanya hannu a kan dokar saboda wata jumla wacce ta tilastawa jam’iyyu zaben ‘yan takaransu kai tsaye a zabubbuka na cikin jam'iyya. Shugaban ya bukaci a cire wannan jamlar kafin ya sanya hannu.
Tuni dai majalisar dattawar kasar ta cira wannan jumlar, wanda kuma ya nuna cewa mai yuwa shugaban ya sanya hannu kan dokar nan da yan kwanaki masu zuwa.
342/