Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar kamfanin na fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa rubtawar ta faru ne a ranar Asabar a lokacinda ma’aikatan suke aikin hakar sinadarin.
Kamfanin COMINAK ya ce har yanzun ba’a san dalilan da suka jawo ruftawarba, amma ya ce an fara gudanar da bincike don sanin musabbabin ruftawar.
Labarin ya kammala da cewa kamfanin 'Orano' na kasar Faransa ne yake da kashi 59% na hannun jari a kamfanin COMINAK, sai kuma kamfanin ENUSA na kasar Espania da kuma SOPAMIN na kasar ta Niger suke da kashi 10% da kuma 31% a jere.
342/