17 Janairu 2022 - 14:44
​Sudan: Mahukuntan Soji Sun Haramta Wa Aljazeera Gudanar Da Aiki A Kasar

Hukumomin kasar Sudan sun sanar da janye izinin da suka baiwa tashar talabijen ta kasar Qatar Al Jazeera.Indan aka yi tuni jim kadan da juyin mulkin soji na ranar 25 ga watan Oktoba a Sudan ,yan sanda sun kama wakilin tashar Al Jazeera da wasu manema labarai dake aiki a wannan kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A lokacin ,ana zargin tashar ta Al Jazeera da yada labaren karya da wasu tsofin faya-faye bidiyo da nufin haifar da rudani a wannan kasa.

A ranar Asabar ne Ministan yada labaren kasar ta Sudan ya aike da wasika da nufin sanar da shugabanin tashar cewa ,ba su da izinin ci gaba da aiki a wannan kasa,wata majiya na zargin tashar da nuna wani bidiyo da ga duk alamu zai iya tunzura jama’a ga tashin hankali.

Tun bayan bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan Albashir da kuma darewa kan kujerar shugabancin kasar da sojoji suka yi, aka fara samun takun saka tsakanin sojojin masu mulki a Sudan da kuma tashar Aljazeera.

342/