Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Majalisar Fatawa ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kira ga daidaikun mutane da cibiyoyi a cikin al'umma da su daina tsunduma cikin harkokin fatawowin addini ba tare da izini ba.
A cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Hadaddiyar Daular Larabawa ta fitar, Majalisar ta yi kira ga al'ummar kasar da kada su buga ko sake buga fatawowin addini wadanda majalisar da hukumomin da ke da ikon bayar da fatawa ba su amince da su ba a kasar.
Majalisar ta ce, ta bayar da wannan umarni ne saboda cin zarafi da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suka yi, kuma wannan kungiya ta masu amfani da yanar gizo za ta fuskanci sakamakon abin da suke aikatawa, musamman yadda ake yin amfani da hakan wajen yada akidar takfir ta ta’addanci da sunan addini, inda ake sauya ma’anar nassi na addini zuwa ma’ana ta ta’addanci.
Majalisar Fatawa ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta jaddada cewa: Wannan yana haifar da yaduwar kyamar musulunci a duniya, da nuna wa musulmi wariya, sakamakon abin da masu tsatsauran ra'ayi daga cikin musulmi suke aikatawa, wanda majalisar ta ce ya sabawa addinin Musulunci da koyarwa, da kuma manufofin zamantakewa na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
342/