Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Turkiya ya nakalto Hassain Alhajj Hassan dan majalisar dokokin kasar Lebanon a bangaren kawancen kungiyar Hizbulla yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da jami’an gwamnatin Lardin Ba’alabak-Hermel a jiya Lahadi.
Alhajj Hassan ya kara da cewa, akwai dalilai na cikin gida wadanda suka hana a fara aikin hakar man fetur da gas na kasar, wadanda daga ciki akwai siyasar tattalin arzikin kasar wacce ta dogaro da kasashen waje, sannan akwai wasu dalilai na waje wadanda suka hada da sharuddan da kasashen waje suka shamfidawa kasar na yin haka.
Hassan ya kammala da cewa, idan da za’a bawa kasar Lebanon damar hakar iskar gas da man fetur nata, da tana iya warware matsalolin tattalin arzikin kasar da dama.
342/