Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mista Kani, ya yi wannan tsokaci ne a karshen tattaunawar tsakanin wakilan kasar Iran da sauran bangarorin dake shafar yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, gabanin fita daga otel din Coburg dake Vienna, inda ake ci gaba da gudanar da tattaunawa kan shirin nukiliyar Tehran.
Mai shiga tsakanin na Iran ya fadawa ‘yan jaridu cewa tattaunawar tana gudana kuma tana kara samun ci gaba.
Iran da sauran bangarorin biyar dake shafar yarjejeniyar nukiliyar da suka hada da Sin, Rasha, Birtaniya, Faransa da Jamus, sun sha gudanar da tattaunawa a zagaye da dama a Vienna, yayin da Amurka ke halartar tattauanwar amma ba kai tsaye ba.
Ana tattaunawar ce, da nufin farfado da yarjejeniyar ta 2015, wacce Washington ta fice daga cikinta a shekarar 2018 karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.
342/