9 Janairu 2022 - 15:48
Mohammadu Buhari Yayi Tir Da Kashe mutum 200 Da Yan Bindiga Suka yi A Zamfara

Mai Magana da yawun shugaban Najeriya ta fuskar yada labarai Malm Garba Shehu ya cewa shugaba buhari ya kadu sosai da samu labarin kisan kare dangi da yan bindiga suka yi wa wasu alumomin a jihar zamfara kana ya nuna cewa hare haren baya bayan nan da yan bindiga ke kaiwa kan mutane da basu ji ba ba su gani ba matake ne na debe kauna saboda matsin lamba da suke fuskanta daga sojojin dake dauke da kayan aiki na tunkarar makiy bil adama ,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace shugaban ya na nan akan bakansa na ganin ganin bayan dukkan ayyukan ta’addanci a kasar ,kana ya bawa alumomin wanan yanki da ma yan Nigeria baki daya na cewa gwamnati bata watsar da su ba tana bakin kokari wajen ganin ta kare rayuwa da dukiyoyinsu fiye da kwanne lokaci a baya

Daga karshe Ya ce da sannu wadannan miyagun zasu zama tarihi domin sojoji nab akin aiki na ganin sun kawar da dukkan wadannan miyagun dake aikata ta’addanci akan bil adama

To sai dai gwammnan jihar ta zamfara Bello matawalle ya rahoton dake nuna cewa mutane 200 aka kashe , yace mutaen 52 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu yankin na Anka.

342/