8 Janairu 2022 - 18:11
​Rwanda Ta Rage Kwanakin Killace Kai Ga Masu Shigowa Kasar Zuwa Kwana Guda

Gwamnatin kasar Rwanda ta rage lokacinda masu shigowa kasar zasu killace kansu bayan shigowa kasar daga kwanaki 3 zuwa kwana guda ko sa’o’ii 24.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar ‘The New Times’ ta nakalto ofishin Firai ministan kasar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa dokar zata fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Jeneru da muke ciki wato ranar Litinin mai zuwa.

Kafin haka dai duk wani mutum da ya shigo kasar ta sama ko kasa dole ne ya bada gwajib cutar Covid 19 Negetive sannan a killace kansa a wani Hotel na kwanaki ukku sannan ya sake bada wani gwajin Negetiuve kafin a barshi ya shiga kasar.

Banda wadannan matakai dai gwamnatin kasar ta Rwanda ta takaita ma’aikatan gwamnati masu zuwa office zuwa kashe 15 % kacal sannan kamfanoni da cibiyoyin kasuwanci masu zaman kansu kuma zuwa kasha 30%.

Gwamnatin ta dauki wadan nan matakai ne bayan da yawan masu kamuwa da cutar suke karuwa. Inda zuwa ranar 6 ga watan Jeneru mutane 1,219 ne suka kamu da cutar.

An yiwa mutane 7,745,536 alluran riga kafin cutar na farko, sannan 5,581,750 sun sami guda biyu a yayinda wasu 273,515 sun sami na uku a duk fadin kasar.

342/