5 Janairu 2022 - 14:23
​Mahmud Abbas : Dole Ne A Bude Sabuwar Hanyar Siyasa Don Kawo Karshen Mamayar Isra'ila

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana cewa, dole ne a bude sabuwar hanyar siyasa domin kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi wa Falasdinu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - M. Abbas ya bayyana hakan ne a karshen taron kwanaki biyu da majalisar jam’iyyar Fatah ta shirya.

Ya kara da cewa, ba za su amince su ci gaba da zama a karkashin mamayar Isra’ila ba, kuma dole ne a kawo karshen mamayar bisa kudurin kasa da kasa. Kalamman nasa na zuwa ‘yan kwanaki kadan bayan ziyarar da ya kai Isra’ila inda ya gana da ministan tsaron Isra’ila Beni Gantz suka kuma sanar da cimma wasu yarjeniyoyi da dama da suka shafi tsaro da tattalin arziki.

342/