Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An dai gudanar da irin wannan taro a birane daban-daban na Iraki da suka hada da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki, inda mutane kimanin miliyan uku suka halarci gangamin, wanda ba a taba ganin makamancinsa a birnin ba.
Baya ga birnin Bagadaza, an gudanar da irin wannan gangamia wasu biranen, da suka hada da Najaf, Karbala da sauransu, inda malamai da jami'ai da sauran dubban al'ummar gari suka halarta.
342/