24 Disamba 2021 - 18:41
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iraki Fu’ad Hussain Na Ziyarar Aiki A Kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir hussain Abdullahiyan da key a taron manema labarai da takwaransa na kasar iraki Fu’ad Hussaini dake ziyara a kasar Iran, ya fadi cewa Iran za ta ci gaba da tattaunawa da kasashen turai 5 gami da kasar Jamsu a birnin Biyanna na ganin an cire mata takunkumi amma fa ba za ta bada rangwame mai yawa baga kasashen turai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya ce a zaman da aka yi a baya na tattaunawar babu wani abin again da kasashen turai suka nuna musamman kasar Faransa na ganin an ta taka muhummiyar rawa wajen ganin tattaunawar ta yi armashi

Yace yayi amanna cewa bangaren kungiyar tarayyar Turai da mai kula da siyasar wajen ta kungiyar suna taka muhimmiyar rawa mai tasiri a wajen tattaunawar ta biyanna na ganin an daukewa kasar iran dukkan takunkumin da aka kakaba mata.

A yau ne ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussain ya kawo ziyara nan birnin Tehran day a jagorancin babbar tawaga domin tattaunawa da mana jami’an gwamnatin kasar , inda ya gana da shugaban kasar Ibrahin Ra’isi.

342/