Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau litinin a gidan gwamnati a nan Tehran, a lokacinda yake ganawa da iyalan shahid Sulaimani da kuma kwamitin shirya juyayin shahadarsa na biyu wanda za’a gudanar a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Har’ila yau shugaba ya kara da cewa shahid Haja Kasim Sulaimani na dukkan musulmin duniya ne, sannan sai da ya gina kansa kafin ya fada cikin ayyuka masu muhimmancin da ya kaddamarwa al-ummar kasashe siriaya da Iraki, sannan yana matukar son Fatimah Zahra(a) diyar manzon All..(s), wacce sau da dama yakan yi tawassuli da ita.
Daga karshe shugaban ya bayyana cewa idan da Shahid Kasim Sulaimani bai kaddamar da ayyukan da yayi a kasashen Iraki da Siriya ba da bamu san irin halin da al-ummar musulmi a yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran kasashen duniya zasu shiga ba.
342/