Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - gwamnatin kasar Siriya ne ya bada wannan labarin, ya kuma kara da cewa makamin wanda aka cillaci daga yankunan tuddan Golan na kasar Siriya wadanda gwamnatin HKI take mamaye da su, ya kashe sojan Siriya guda da misalign karfe 12:50 na safiyar yau Alhamis.
Labarin ya kara da cewa rundunar sojojin kare sararin samaniyar kasar Syriya sun samu nasarar kakkabo da dama daga cikin makamai masu linzami wadanda sojojin HKI suka harba daga yankin na tuddan Golan.
HKI ta mamaye yankin tuddan Golan na kasar Syriya ne a yakin shekara ta 1967 tsakanin kasashen Larabawa da kuma haramtacciyar kasar.
342/