15 Disamba 2021 - 14:13
Iran Zata Sayar Wa Senegal Da Motocin Tasi Guda 2000

Kamfanin kera motoci na kasar Iran (Iran Khudro) ya kulla yarjejeniya da gwamnatin kasar Senegal don seyarwa kasar motocin haya samfurin Thaman har 2000.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Majiyar muryat jumhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa an gudanar da bikin sanya hannu a kan yarjejeniyar sayan motocin ne a jiya Laraba a birnin Daka babban birnin kasar ta Senegal, inda Hassan Zakiri shugaban kamfanin kera motoci na kasar Iran ya sanya hannun a madadin kamfani.

Har’ila yau a bikin na jiya laraba kamfanin kera motoci na kasar Iran ya mikawa gwamnatin kasar ta Senegal makullan motoci 48 wadanda za’a yi amfani da su tashar sauka da tashin jiragen sama na birnin Daka.

342/