Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - nakalto shugaban yana cewa za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a waten Dicemba na shekara mai zuwa. Reuters ya kara da cewa shugaba Kais Saeid ya bayyana haka ne a wani jawabin da ya yi mutanen kasar a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa a cikin watan Yuni na shekara mai zuwa za’a kammala aikin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar, wato wata guda kafin a gudanar da zaben raba gardama a kansa.<p "="">Har’ila yau shugaban ya bayyana cewa za’a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 17 ga watan Dicemba na shekara ta 2022 kuma majalisar ce zata maye gurbin majalisar da ra rasu. Har yanzun dai ba’a ji ta bakin jam’iyyun adawar kasar wadanda suke ganin shugaban yayi masu juyin mulki ne kawai.
342/