11 Disamba 2021 - 13:38
An Kashe Mutane 404 A Cikin Watan Nuwamba Sakamakon Hare- hare A Nijeriya

Rahoton da kamfanin Beacon Consulting ya fitar game da sha’anin tsaro a Nigeria ya nuna cewa a cikin watan Nuwamba da ya gabata hare haren yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya kara muni sosai inda aka kashe mutane 404 a jihohin 28 na Najeriya acikin kana nan hukumomi 115,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ya ci gaba da cewa kai hare-haren ya karu da kasha 38 cikin dari a watan Nuwamba idan aka kwatanta da sauran watanni baya da suka gabata, inda aka sace mutane 363 domin karbar kudin fansa.

Sai dai rahoton ya nuna cewa wadannan alkaluman da aka fitar ya hada da mutane da aka kashe sakamkon hare-haren yayan kungiyar Boko Haram, da kuma yan fashin daji a arewa masu yammaci da tsakiyar kasar.

Daga karshe a rahoton

an shawarci mahukumtan kasar da su kasance cikin shirin ko ta kwana na yi yuwar

kai hare –haren ramuwar Gayya daga yan bindigan a yankin Arrewa maso tsakiy da

Arewa masu Yammaci saboda Nasarori da Jami’an tsaro ke samu aka maharan.

342/